Gwamnatin Tarayya ta ce, za ta samar da titin dogo domin sufurin jirgin ƙasa a ƙwaryar birnin Kano da ke arewacin ƙasar, wanda zai laƙume naira triliyan 1 da rabi, a kamar yadda shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar wakilai Abubakar Kabir Abubakar ya bayyana.
Jaridar DailyTrust ce ta ruwaito ɗan majalisar yana bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyin ƴan jarida a Kano, inda ya ce shirin zai magance matsalolin da ake fuskanta a ɓangaren sufuri a jihar.
“Duk wanda ya yi tafiya zuwa Turai ko Asiya zai ga irin waɗannan jiragen ƙasan kuma zai san muhimmancin su. Shirin zai matuƙar taimakawa tattalin arziƙin jihar idan an kammala.”
Ya kuma ce Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da muhimman abubuwan ci gaba a arewacin ƙasar, kama daga ababen more rayuwa, da fannin lafiya, da noma da ilimi da kuma tsaro, ba kamar yadda mutane da dama ke zargi ba na cewa Tinubu ya mayar da yankin saniyar ware.