fidelitybank

Gwamnatin tarayya ta yi sulhu da ƴan Bindiga – Mazauna Birnin Gwari

Date:

Al’ummar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna, sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta faɗaɗa shirin sasanci da ƴanbindiga da aka yi a yankin zuwa sauran jihohin da ke fama da matsalolin rashin tsaro.

Wannan kiran na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ƙungiyar ci gaban yankin masarautar Birnin Gwari wato Birnin Gwari Birnin Gwari Emirate Progressives Union (BEPU), wadda shugabanta Isah Muhammad ya sanya wa hannu.

Sanarwar ta ce al’ummar yankin suna godiya da zaman lafiya da suka fara samu a sanadiyar sasancin, “amma muna kira da a faɗaɗa shirin zuwa sauran jihohin da suke fama da matsalar ƴanbindiga irin su Neja da Zamfara da Katsina da Sokoto domin hakan ne zai wanzar da zaman lafiya a faɗin ƙasar.”

Sanarwar ta kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha da su samar da ababen more rayuwa a yankin na Birnin Gwari, “akwai buƙatar a gyara titin Birnin Gwari zuwa Kaduna da na zuwa Funtua da zuwa Neja da na zuwa Tegina, wanda ya sada yankin da kudancin Najeriya.”

BEPU ta kuma kira ga kamfanonin sadarwa irin su MTN da Airtel da su dawo da hanyoyin sadarwarsu da suka katse a baya a yankin, sannan ƙungiyar ta yi kira a kafa jami’ar nazarin ayyukan noma saboda yadda ake noma a yankin.

Yankin Birnin Gwari ya daɗe yana fama da matsalar tsaro, amma cikin ƴan kwanakin nan an fara samun zaman lafiya, inda harkokin kasuwanci da noma suka fara komawa yadda ya kamata bayan wani shirin sasanci da ƴanbindiga da gwamnatin ta jagoranta.

sun newspaper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...
X whatsapp