fidelitybank

Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamiti a kan baiwa ƙananan hukumomi hakkin su

Date:

Gwamnati ta ƙaddamar da wani kwamiti mai mutum 10 da zai duba shirin aiwatar da hukuncin da Kotun Ƙolin ƙasar ta yi game da bai wa ƙananan hukumomi ‘yancin gashin-kai.

A ranar 11 ga watan Yulin da ya gabata ne Kotun Ƙolin ta yanken hukuncin cewa matakin da gwamnonin jihohi ke ɗauka na ci gaba da riƙe wa ƙananan hukumomi kuɗaɗen gudanarwasu ya saba wa doka.

Makonni biyu da yanke wannan hukuncin Sakataren Gwamnati Sanata George Akume, ya kafa kwamitin domin aiwatar da wannan hukuncin.

Kwamitin da ya ƙunshi ministan kuɗi da babban lauyan gwamnati kuma ministan shari’a da ministan kasafin kudi da tsare-tsare, da babban akanta kuɗi na ƙasa da gwamnan babban bankin Najeriya da babban sakatare a ma’aikatar kuɗi da tara haraji da wakilan gwamnonin jahohi da kuma na kananan hukumomi.

Darakta watsa labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya, Segun Imohiosen, ya bayyana cewa babban muradin da kwamitin ya sanya a gaba shi ne tabbatar da an bai wa duka ƙananan hukomi 774 na ƙasar, ‘yancin gashin kai, ta yadda za su yi amfani da kuɗinsu ba tare da fuskantar katsalandan daga gwamnonin jahohi ba, kamar yadda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya saka wa muradin ganin an bi turbar da kundin tsarin mulkin Najeriya ya sharɗanta.

A tsarin rabon tattalin arziki da kuɗaɗen gudanarwar wata-wata gwamnatin tarayya na samun kashi 52.68 cikin 100, jihohi masu kashi 26.72, yayin da ƙananan hukumomi ke samun kashi 20.60 cikin 100 na kuɗin.

Masana dai na ganin za a samu sauyi ga bunƙasar ƙananan hukumomi musamman idan har suna da damar tafiyar da kuɗaɗensu, muddin babu wata hanya ta zangon-ƙasa da aka bijiro da ita, kasancewar kuma su ne suka fi kusa da talakawa.

Sai dai duk hasashen samun sauyin bayan hukuncin Kotun Ƙolin, wasu na bayyana shakku kan yadda za a tabbatar ba a yi facaka da kuɗaɗen ba kamar yadda aka yi a baya ba.

vanguard news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...
X whatsapp