Biyo bayan afkuwar ambaliyar ruwa da ta afku a jihar Borno, gwamnatin tarayya ta amince da kafa wani kwamitin kwararru da zai duba dukkan madatsun ruwa da ake da su a kasar.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Ibrahim Mohammed, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya, FEC, wanda shugaba Bola Tinubu ya jagoranta.
Ya ce hukumar ta FEC ta amince da kwamitin kwararrun ne domin a samu damar shawo kan matsalolin da ke haifar da ambaliya a kasar.
A cewar Ministan Yada Labarai, gwamnati ba ta damu ba cewa wasu madatsun ruwa da aka yi shekaru da yawa na iya bukatar kulawa, don haka akwai bukatar kwamitin kwararru ya duba dorewarsu.