Gwamnatin tarayya ta ce, cin amanar kasa ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, LP, Peter Obi, ya tunzura mutane zuwa tashin hankali sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Ministan yada labarai da al’adu Lai Mohammed ne ya bayyana haka a birnin Washington DC a lokacin da yake ganawa da kungiyoyin yada labarai na duniya.
NAN ta ruwaito cewa, Mohammed ya zuwa yanzu yana mu’amala da kafafen yada labarai kamar Washington Post, Muryar Amurka, Associated Press da Mujallar manufofin kasashen waje.
A daya daga cikin mu’amalar da aka yi, ministan ya ce, ba daidai ba ne Obi ya nemi a yi masa hukunci a kotu kan sakamakon zaben da kuma tada zaune tsaye.
“Obi da mataimakinsa, Datti Ahmed, ba za su iya yi wa ‘yan Najeriya barazana cewa idan aka rantsar da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu na jam’iyyar APC a ranar 29 ga watan Mayu, zai kawo karshen mulkin dimokuradiyya a Najeriya.
“Wannan cin amana ne. Ba za ku iya zama kuna gayyatar tayar da hankali ba, kuma abin da suke yi ke nan.
“Maganar Obi na mutum ne mai yanke kauna, ba shi ne dan dimokradiyya da ya yi ikrarin zama ba.
“Bai kamata dan dimokradiyya ya yi imani da dimokradiyya ba kawai idan ya ci zabe,” in ji Mohammed.