Gwamnatin tarayya ta ci tarar kamfanin taba sigari na Birtaniya mai suna British American Tobacco da sauran rassan kamfanin dala miliyan 110.
Hukumar kare haƙƙin masu sayen kaya ta Najeriya ce ta bayyana cin tarar a wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce an ɗauki matakin ne saboda zargin keta dokar hukumar da dokar taƙaita harkokin taba sigari ta ƙasa.
Hukumar ta ƙara da cewa ya zama dole kamfanin ya mutunta dokoki sannan kuma za a riƙa bibiyar ayyukansa tsawon wata 24, kuma ya bayar da tabbaci a rubuce na kiyaye dokoki da wayar da kai game da kare lafiyar al’umma da kuma rage taba sigari.
“Domin samun masu kamfanin su cika ƙa’idoji ƙarƙashin dokar izini, hukumar ta janye tuhume-tuhumen da ake yi wa kamfanin da kuma wani ma’aikacinsa dangane da yunƙurin hana gudanar da bincike a kamfanin da kuma rashin ba da haɗin kai domin aiwatar da aikin, kamar yadda hukumar ta ce.
A cewar hukumar, ta ƙaddamar da bincike tare da ƙwace wasu kayayyaki bayan samun izinin watan babbar kotun tarayya a rassan kamfanin na BAT a ranar 25 ga watan Janairu.
Hukumar ta bayyana cewa ta tattara ta kuma samu isasshiyar hujja daga binciken ƙwaƙwaf da aka yi na kafofin sadarwa da sauran bayanai da aka tattaro sakamakon binciken da kuma shaidun da aka gano daga sahihan majiyoyi yayi da kuma bayan binciken.
Hukumar ta ƙara da cewa a shirye take ta inganta da kuma tabbatar da tsaftace kasuwanni domin kare masu sayen kayayyaki.


