Gwamnatin tarayya ta amince da wasu sabbin manufofi da za su taimaka wa ƙasar wajen magance ƙaurar ma’aikatan lafiya zuwa wasu ƙasashe, domin rage ƙalubalen da ɓangaren lafiya na ƙasar ke fama da su.
Ministan Lafiya, Ali Pate ne ya sanar da hakan a ranar Litinin a shafin sada zumuntasa na X, yana mai jaddada ƙudurin gwamnati na magance ƙaurar ƙwararrun likitoci da ma’aikatan lafiya daga kasar.
Shugaba Bola Tinubu ne ya jagoranci zaman majalisar zartarwa ta tarayya a fadar shugaban kasa da ke Abuja, inda aka amince da manufar.
Najeriya na fama da yawan ƙaura da likitoci da kuma malaman jinya ke yi zuwa ƙasashen ƙetare domin neman albashi mai tsoka.
Lamarin ya jefa ɓangaren lafiya na ƙasar cikin mummunan yanayi, inda ake kokawa kan ƙarancin likitoci da sauran malaman lafiya.
“Wannan manufar an samar da ita ne ba kawai domin magance ficewar da masana kiwon lafiya ke yi zuwa ƙasashen ƙetare ba ne, har ma da aiwatar wani muhimmin tsari da zai kawo gyara a ɓangaren lafiya na ƙasar,” in ji Pate.
Ya kara da cewa manufar ta tanadi samar da ma’aikata masu inganci waɗanda za su samu tallafi mai kyau da kuma amfani da su yadda ya kamata domin biyan buƙatun kiwon lafiya na daukacin ‘yan Najeriya.
Babban makasudin sabuwar manufar ita ce karfafa dawowa da ƙwararrun likitocin Najeriya daga kasashen waje
“Wannan manufar ta kuma bayar da shawarar yin yarjejeniya da sauran ƙasashe, don tabbatar da cewa Najeriya ta amfana da musayar ma’aikatan kiwon lafiya,” in ji Ministan.
Bugu da ƙari, manufar ta jaddada mahimmancin samun daidaito a rayuwar ma’aikatan kiwon lafiya da ayyukansu na yau da kullum.