Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a zaɓen da ya wuce, Peter Obi, ya ce da alama ministan yaɗa labarai, Lai muhammad yana son rataya masa jakar tsaba.
Ya ce ministan yana wannan yunƙuri ne game da wata tattaunawar wayar salula tsakanin Obi da Bishop David Oyedepo, wani babban limamin Kirista na majami’ar Living Faith Church, wadda ta janyo muhawara mai zafi da ce-ce-ku-ce.
Wannan ne karon farko da Peter Obi ya fito ya maida martani game da lamarin, tun bayan kwarmata tattaunawar.
Ya wallafa martanin ne a shafinsa na Tuwita.
Ɓullar sautin dai ya janyo zazzafar muhawara a tsakanin al’ummar Najeriya musamman a shafukan sada zumunta, inda masu adawa da shi ke zargin sa da cewa saɓanin iƙirarin da yake yi a fili, shi ma dai ɗan siyasa ne da ke amfani da ƙabilanci da bambanci addinai don cimma biyan buƙatarsa..
Shi dai Mista Lai Mohammed ya zargi Peter Obi da cin amanar ƙasa, kasancewar a tattaunawar an ji yadda ɗan takarar yake alaƙanta siyasarsa, tamkar wani yaƙi na addini tare da tabbatar wa limamin kirista cewa, (Kiristoci) ba za su yi da na sanin goya masa baya ba.
Har ma Obi yana roƙon malamin ya taimaka masa wajen nema masa goyon bayan mabiya addinin kirista da ke kudu maso yammacin Najeriya da kuma shiyyar arewa ta tsakiyar ƙasar.
Peter Obi ya ce abin takaici ne yadda ake ta yunƙurin ɓata masa suna da kuma kasancewar hakan na zuwa ne daga wajen ministan gwamnati.
A cewar Peter Obi, bai taɓa yin wata magana ko kuma ƙarfafa gwiwar a yi wa Najeriya maƙarƙashiya ba sannan ya ce bai taɓa ɗaukar nauyi, ko ma furta wani mummunan abu game da Najeriya ba.