Gwamnatin tarayya na neman sake nazarin dokokin duniya domin kare wayoyin ƙarƙashin teku inda ta ce za ta tattauna da ƙasashe domin hanzarta yunƙurin.
Ministan yaɗa labarai na ƙasar, Bosun Tijjani ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.
Tun ranar Alhamis ne, abokanan hulɗar kamfanonin sadarwa da bankuna suka fuskanci matsalar sadarwar intanet saboda katsewar wayoyin ƙarƙashin tekun Atalantik da ke Cote D’Ivoire ta gaɓar tekun yammacin Afirka, lamarin da ya gurgunta harkokin cinikayya ta intanet da sadarwar intanet.
Kamfanin wayoyin ƙarƙashin teku na MainOne ya ce zai ɗauki kusan mako biyu kafin gyara matsalar da ta lalata intanet a Najeriya da Ghana da Cote D’Ivoire da Senegal da wasu ƙasashen yammacin Afirka da na gabashin yankin a kwanaki huɗun da suka gabata.
Kamfanin ya danganta matsalar ga ayyukan masunta da girgizar ƙasa da zaizayewar laka da kuma tangarɗar na’ura.
Ministan a saƙon nasa ya ce matsalar da aka samu za ta taimaka wajen samar da hanyoyin inganta sadarwa a Najeriya.
Ya kuma yaba da shugabancin kamfanin na MainOne da sauran kamfanonin sadarwa a ƙoƙarinsu na taƙaita tasirin katsewar.
Ya kuma bai wa mutanen da ke ci gaba da fuskantar matsala tabbacin cewa hukumar sadarwar Najeriya NCC tana aiki da muhimman masu ruwa da tsaki domin warware matsalar a ƙanƙanin lokaci.