Ƙungiyar ɗalibai Musulmi ta Najeriya (MSSN), ta rubuta takaddar ƙorafi ga gwamnatin tarayya a kan wasu littattafai da ake koyarwa a makarantu cewa, suna ɗauke da abubuwa za su bata tarbiyya da addinin yara.
A wasikar da kungiyar shiyya ta biyu (B-Zone) ta aika wa Ministan Ilimi Adamu Adamu, ta ce wasu daga cikin littattafan na koyar da lissafi da Ingilishi da kimiyyar zamantakewa (Social Sciene) da ake amfabi da su a yawancin makarantun sakandire suna dauke da abubuwa na koyar da badala da batsa, wadanda ta ce an tsara domin an gurbata dabi’ar matasa dalibai.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, wasikar wadda ke dauke da koken babban jami’in kungiyar Qaasim da Babban Sakatarenta Abdul Jalil Abdur Razaq suka sanya wa hannu ranar 15 ga watan nan na Mayu.
Kungiyar ta MSSN ta ce wasu daga cikin littattafan na yada ilimin zubar da ciki da ludawi da madigo da amfani da kororon roba da sauran dabi’u da kungiyar ta ce ba su dace da matasa ba domin za su bata musu tarbiyya ta addini da kuma al’ada.
saboda haka kungiyar ta bukaci ma’aikatar ilimi ta Njaeriya ta gaggauta gudanar da bincike a kan dukkanin littattafan da ake amfani da su a makarantun kasar ta tabbatar ba sa dauke da abubuwan da za su bata tarbiyyar dalibai matasa.
Wasu daga cikin littattafan sun hada da: Basic Science Junior Secondary School Razat Publishers, 2018 edition, (for JSS3); New Concept English for Senior Secondary Schools for SSS2, Revised edition (2018 edition); Active Basic Science, 2014 edition and Basic Science & Technology for Junior Secondary School 1, 2 and 3.