fidelitybank

Gwamnatin Taliban ta sanya dokoki ga matan Afghanistan

Date:

Gwamnatin Taliban a kasar Afghanistan ta sanar da cewa, duk macen da ke son yin tafiya, sai ta kasance tare da wani dangi na kusa da ita.

Masu motocin za su baiwa matan da ke sanye da hijabi na Musulunci kawai abin hawa, inji jagorar da ma’aikatar inganta nagarta da rigakafin ta bayyana.

Mai magana da yawun ma’aikatar, Sadeq Akif Muhajir ya bayyana hakan yayin da ya ke magana da kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Lahadi cewa, dole ne ya kasance dangi na kud da kud, “Bai kamata a ba matan da ke tafiya fiye da mil 45 (kilomita 72) ba idan ba su tare da wani dangi na kusa ba”.

Sabon umarnin ya zo ne makonni bayan da ma’aikatar ta bukaci gidajen talabijin na Afganistan da su daina nuna wasan kwaikwayo na tallan sabulu da ke nuna mata ‘yan wasan kwaikwayo.

Ma’aikatar ta kuma yi kira ga mata ‘yan jarida na TV da su sanya hijabi yayin gabatar da su.

Ministan ya kara da cewa, za a kuma bukaci mata masu neman abin hawa su sanya hijabi. Umarnin na ma’aikatar ya kuma bukaci mutane da su daina kida a cikin motocinsu.

A halin da a ke ciki, ba a fayyace fassarar da Taliban ta yi wa hijabi ba, saboda yawancin matan Afghanistan sun riga sun sanya hijabi.

Tun bayan da kungiyar ta Taliban ta karbi mulki a watan Agusta, ta kakaba takunkumi iri-iri kan mata da ‘yan mata, duk da cewa sun yi alkawarin kafa wata doka mai sassauci idan a ka kwatanta da mulkinsu na farko a shekarun 1990.

legit.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp