Gwamnatin Sudan ta ce, ba za ta amince da cigaba da zaman Volker Perthes ba, mutumin da Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta tura a matsayin jakadanta a kasar.
Shugaban sojojin Sudan – kuma mai rike da mulkin ƙasar – Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya zargi Mista Perthes da sake assasa rikici a ƙasar, inda ya nemi a gaggauta sauya shi.
Kafin soma yaƙi tsakanin sojojin Sudan da dakarun rundunar RSF, an yi ta samun zanga-zangar adawa da MDD a Sudan bayan zargin katsalandan a harkokin kasar daga ƙetare.