fidelitybank

Gwamnatin Sokoto ta sassauta dokar hana fita

Date:

Gwamnatin jihar Sokoto, ta sassauta dokar hana fita ta sa’o’i 24 da ta kafa a jihar, sakamakon zanga-zangar da ta ɓarke kan kama waɗanda ake zargi sun kashe ɗalibar da ake zargi ta yi ɓatanci ga Manzon Allah S.A.W.

Daruruwan musulmi ne suka fito kan titi suna neman a sako wadanda ake zargi da hannu a kisan wata daliba da ake zargi da yin batanci ga addinin Musulunci.

Amma zanga-zangar ta rikiɗe zuwa tashin hankali tare da kona tayoyi a kan tituna, da wawashe shaguna da kuma toshe manyan tituna kafin jami’an tsaro suka harba hayaki mai sa hawaye, domin tarwatsa masu zanga-zangar. Lamarin da ya sa gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal ya kafa dokar hana fita.

A wata sanarwa daga kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na jihar Sokoto, Isah Bajini Galadanci ya fitar, ya ce, bayan nazarin yanayin tsaro, an sassauta dokar ta bacin, inda ta koma daga magariba zuwa wayewar gari.

A cewar gwamnati, an yi hakan ne domin ba mutane damar gudanar da harakokinsu na yau da kullum. In ji BBC.

Gwamnatin jihar, duk da haka, ta yi kira ga al’ummar Sokoto da su kasance masu zaman lafiya, tana mai cewa ”ba za a amince da duk wanda ya keta doka da oda ba”’.

nigerianewspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp