Gwamnatin jihar Sokoto ta sake ƙaddamar da hukumar Hisbah a faɗin jihar, domin yaƙi da gurɓacewa tarbiyyar al’umma a jihar.
Cikin wani saƙo da gwamnan jihar, Ahmad Aliyu ya wallafa a shafinsa na X, ya ce ya sake kafa hukumar ne saboda irin gudunmowar da take bayarwa wajen yaƙi da gurɓacewar tarabiyya.
Bayanan hoto,Shugaban hukumar Hisbah na jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daura na daga cikin mutanen da suka halarci taron ƙaddamarwar
Gwamnan ya kuma ya buƙaci sabbin jami’an hukumar da su gudanar da ayyukansu bisa doka ba tare da cin zarafin kowa.
Ahmad Aliyu ya ce sabuwar hukumar da ya kafa ba wai za ta maye gurbin sauran hukumomin tsaro ba ne, sai ma dai ta taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu na kare rayuka da dukiyoyi.
Dokokin jihar sun bai wa hukumar damar kama masu laifi tare da hannun ta su ga jami’an ‘yansanda domin a gurfanar da su a gaban Kotun Shari’a.
Gwamnan ya kuma yi kira ga al’ummar jihar su bai wa sabuwar hukumar goyon bayan datake buƙata wajen gudanar da ayyukanta.