Gwamnatin jihar Sokoto ta sanar da yunƙurinta na fara sayar da shinkafa da sauran kayayyakin abinci, inda za ta sayar da su da ragowar kashi 55 na farashin kayayyakin abincin, wanda da ta sayo na naira biliyan 14.
Gwamna Ahmed Aliyu ne ya sanar da hakan a lokacin da yake ƙaddamar da kwamitin bibiya da sa ido a kan sayar da kayan abinci a yau Litinin, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Gwamnan ya ce sun ɗauki wannan matakin ne domin rage wa mutane raɗaɗdin da suke ciki na tsananin rayuwa tun bayan cire tallafin man fetur, inda ya ce abincin zai kai dukkan mazaɓun jihar guda 244.
“Ku guji sanya bambancin siyasa ko addini wajen sayar da kayayyakin abincin. Wannan abinci ne na dukkan ƴan jihar Sokoto.” in ji shi.
Ya kuma ƙara da cewa gwamnatinsa za ta cigaba da aiwatar da tallafi irin haka har zuwa lokacin da tattalin arzikin ƙasar zai bunƙasa.
A ƙarshe ya yi kira ga masu hannu da shuni a jihar da kamfanoni, da su taimaka wajen rage wa mutane halin raɗaɗin da mutane suke ciki.