Gwamnan jihar Oyo, ‘Seyi Makinde, ya bada tabbacin cewa gwamnatin sa za ta sassauta ayyukan Hajji tare da sanya sansanin Alhazai na Olodo ya zama mazaunin mahajjata.
Gwamnan wanda ya ke jawabi ga maniyyata 151 da suka zo gabatar da koke game da ayyukan Hajji na 2022 a ofishin sa, ya bayyana cewa, jinkirin jigilar su ya biyo bayan kason da hukumar alhazai ta kasa ta ba jihar.
Wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan, Taiwo Adisa, ya fitar, ta ruwaito shi yana cewa, zai duba matsalolin da suke fuskanta tare da samar da mafita.
Ya kara da cewa, bayanan da suka zo masa na cewa hukumar alhazai ta kasa ta yi alkawarin dawo da ma’aikatun farko guda 150 da ta dakatar da su zuwa jihar, inda ya ce da zarar an kammala hakan, gwamnatinsa za ta tabbatar da an dauke su cikin gaggawa.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa, gwamnatinsa za ta nemo hanyoyin gyara ababen more rayuwa a sansanin Hajji dake Olodo, Ibadan, inda ya kara da cewa, yin hakan zai sa sansanin Alhazai ya zama wurin zama ga mahajjata.
- Ya ce: “Gaskiya ina magana, na lura da dukan koke-kokenku. A daren jiya na yi taro da kwamitin don fahimtar yadda muka shiga wannan matsalar. Kamar yadda kuka ce, adalci yana da gaskiya kuma na gaya musu cewa, ƙarin adadin 150 bai kamata a haɗa shi da mutanen da ke cikin jerin ba. Don haka, na yarda da ku.
- “Na samu labari daga wani mataimaka na a ‘yan mintoci kadan baya cewa Hukumar Alhazai na kokarin dawo mana da mutane 150. Kuskuren da ya faru shi ne cewa babu wanda ya kamata a cire daga cikin 629 da aka haɗa a cikin rukunin farko.