Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya ce gwamnatinsa ta sayo kananan jiragen sama marassa matuka domin taimaka wa hukumomin tsaro bin diddigi da gano masu aikata miyagun laifuka.
Gwamnan ya sanar da haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin sabon Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Frank Mba da sabon kwamandan rundunar atilare ta 35 ta sojin kasa na Najeriya, da ke Alamala a Abeokuta Birgediya-Janar Mohammed Aminu a ofishinsa da ke Abeokuta, jiya Alhamis..
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Gwamna Abiodun ya ce jiharsa ta yi hadain guiwa da makwabciyarta Oyo inda suka kakkafa cibiyoyin tsaro domin a kan babban titin Lagos-Ibadan domin magance matsalar satar mutane da sauran miyagun laifuka.
Haka kuma ya ce rundunar ‘yan sandan jihohin biyu suna wani aiki na hadin guiwa inda suke shiga dazukan yankin domin farautar masu aikata laifi.