A ranar Talata ne gwamnatin Nijar, ta yi watsi da sabuwar tawagar diflomasiyya daga kasashen Afirka da nufin maido da tsarin mulkin kasar bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yuli.
NAN ta ruwaito cewa gwamnatin mulkin sojan ta ki amincewa da matsin lamba daga Amurka da Majalisar Dinkin Duniya na zuwa kan teburin tattaunawa.
Shugabanin kasashen kungiyar ECOWAS, na shirin gudanar da wani taro a yau Alhamis, domin tattaunawa a kan takaddamar da ke tsakaninsu da gwamnatin mulkin sojan Nijar, wadda ta bijirewa wa’adin ranar 6 ga watan Agusta na maido da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum.
Za a tattauna yiwuwar shiga tsakani na sojoji amma kungiyar ECOWAS ta ce matakin karshe ne.
Mujallar Jeune Afrique ta kasar Faransa ta bayyana cewa kungiyar tarayyar Afrika AU ta aike da tawagar hadin gwiwa tare da wakilan Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar ECOWAS zuwa Nijar a ranar Talatar da ta gabata amma gwamnatin mulkin sojan kasar ta hana su izinin shiga kasar, lamarin da ya rufe sararin samaniyar Nijar.