Kusan kowa a Ukraine na cikin tashin hankali sakamakon hare-hare da Rasha ta ƙaddamar a ƙasar.
A babban birnin Kasar Kiv, ana ta jin karar jiniya domin yi wa jama’a gargadi , yayin da jerin gwanon motoci ke layin barin birnin, sannan kuma cincirindon mutane na ta ƙoƙarin neman mafaka a tashoshin jiragen ƙasa na ƙarƙashin kasa.
Akwai ƴan Najeriya da dama da ke zaune a Ukraine kuma wasunsu sun shaida wa BBC cewa suna cikin tashin hankali.
BBC ta tuntuɓi Firdausi Muhammad Usman, ƴar Najeriya da ke karatu a Ukraine kuma ta ce, gwamnatin Najeriya ta taimaka ta dawo da su gida Najeriya daga Ukraine.