Amurka ta yi kira ga hukumomi a Najeriya su gurfanar da mutanen da suka yi wa masu zabe barazana, inda suka yi yunkurin hana su jefa kuri’a a zaben gwamna da yan majalisar dokoki na jihohi da aka yi ranar Asabar.
Ofishin jakadancin Amurka ta ce, an samu irin wannan matsala a Legas da Kano da wasu jihohin da aka gudanar da zaben.
Karanta Wannan:Â Hukumar zabe ta gaggauta sauya zaben Kano – APC
Ita ma tawagar Tarayyar Turai da ta sa ido kan zaben ta ce, jihar Legas na daga cikin jihohin da aka samu tashin hankali da satar akwatin zabe da kuma yi wa masu zabe da ma’aikatan zabe da masu sa ido da kuma yan jarida barazana.
Kimanin mutum 21 tawagar ta EU ta ce an kashe sakamakon tashin hankalin da aka yi a lokacin zaben.