Najeriya ta karɓo bashin dala miliyan 747 daga bankunan zuba jari ƙarƙashin jagorancin Deutsche Bank domin gudanar da wani ɓangare na aikin kilomita 700 na babban titin gaɓar teku.
Kakakin ma’aikatar kuɗin ƙasar, Mohammad Manga ya ce ba shin shi ne irinsa na farko mafi girma da ƙasar ta ciyo domin aikin titi.
Kashin farko na babban titin da aka yi da kuɗin ramcen da aka karɓo ya kai kilomita 47.47 a cewar Manga.
Ana sa ran aikin titin – wanda zai ɗauki shekara takwas ana yi zai laƙume kuɗi kimanin dala biliya 11.
Babban titin zai haɗa cibiyar kasuwancin ƙasar Legas da birnin calabar mai tashar jiragen ruwa da ke kudu maso kudancin ƙasar.