Kotun kwadago ta zartar da hukuncin cewa, matakin da gwamnati ta dauka kan kungiyar Malaman Jami’a na kin biyan mambobinta da suka shiga yajin aiki albashi yana kan doka.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Shugaban kotun mai shari’a Benedict Kanyip, ne ya bayyana hakan yayin da yake sanar da hukuncin, inda ya ce gwamnatin tarayyar tana da ikon rike albashin ma’aikatan da suka shiga yajin aiki.
Sai dai kuma a bangaren tsarin biyan albashi kotun ta zartar da cewa, ya saba wa tsarin ƴancin cin gashin kai na jami’a a tilasta wa malaman shiga tsarin nan na biyan labashi na, IPPIS, saboda malaman suna da ƴancin zabar yadda za a biya su albashinsu.
A ranar 14 ga watan Fabarairu ne ASUU ta shiga yajin aiki, wanda ya kai wata takwas a kan neman kyautata yanayin albashi da inganta tsarin ilimin jami’a da sauran bukatu.
Yajin aikin ya sa daliban kasar da dama zaman gadi yayin da gwamnati ta kafe cewa ba za ta biya malaman albashi ba tsawon lokacin da suka yi yajin aikin.


