Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani ya bai wa al’ummar musulmi da kirista da ke jihar tabbacin cewa gwamnatinsu za ta yi wa kowa adalci.
Sanata Uba Sani ya bayyana hakan lokacin da ya halarci taron waƙoƙin kirsimeti da ƙungiyar kiristoci ta Najeriya CAN ta shirya a cocin Ecwa, reshen Kaduna.
An shirya taron domin rera waƙe-waƙen yabo da yin addu’oi domin samun zaman lafiya da haɗin kai a jihar Kaduna.
A jawabinsa, shugaban ƙungiyar CAN reshen jihar Kaduna, Rev Dr John Joseph Hayab ya yaba wa gwamnatin Kaduna saboda yadda ta maido da yadda da kuma yadda take sa kowa cikin tsarin tafiyar da shugabancinta.
Gwamna Uba Sani ya ƙara da cewa “za su yi duk mai yiwuwa domin ganin an samu ci gaba a kowane ɓangare na jihar Kaduna musamman yankunan karkara.”
Ya kuma ce cikin ƴan kwanaki masu zuwa, gwamnatinsu za ta fara ayyukan shimfiɗa tituna a wasu kananan hukumomi da ke kudancin jihar kamar yadda suka yi a arewacin jihar.