fidelitybank

Gwamnatin Mali ta bayar da umarnin a cire tashar Faransa daga kasar ta

Date:

Gwamnatin ƙasar Mali karkashin jagorancin sojin kasar ta bayar da umarnin cire tashar talabijin na France 2 daga yaɗa shirye-shiryenta na tsawon watanni hudu bayan da tashar ta watsa wani labarin da hukumomin kasar suka dauka a matsayin “neman uzuri ga masu aikata ta’addanci”.

Labarin, wanda ya shafi yanayin tsaro a Mali, an watsa shi ne a ranar 20 ga watan Janairu.

Hukumar Kula da Sadarwa ta Mali (HAC) ta zargi gidan tashar da “ingiza aikata ta’addanci” ta hanyar kwatanta “karfin kungiyoyin ta’addanci” da na sojojin ƙasar.

HAC ta kuma zargi tashar da gaza jin ta-bakin mahukuntan Mali kafin watsa labarin da kuma “mummunan keta dokar aikin jarida.

Wannan dai ba shi ne mataki na farko da ƙasar Mali ta dauka a kan kafafen yada labaran Faransa ba.

A shekarar 2022, gwamnatin mulkin soja ta dakatar da France 24 da Radio France Internationale.

Dangantaka dai tsakanin Mali da tsohuwar ƙasar da ta yi mata mulkin mallaka, Faransa ta tabarbare tun bayan da shugaban mulkin sojan kasar Kanar Assimi Goita ya kwace mulki a shekara ta 2021.

national news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Za a fuskanci ambaliya a wasu jihohin – NIMET

Hukumar kula da yanayi ta NiMet, ta ce akwai...

Za mu mayar wa da Isra’ila martani mai tsanani – Iran

Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi alwashin mayar...

Ba za mu taɓa barin Iran ta ƙera makamai masu linzami ba – Isra’ila

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce burin ƙasarsa shi...

Isra’ila ta buga gangar yaƙi – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya ce...

Iran ta na cigaba da luguden makami mai Linzami cikin Isra’ila

Ana ci gaba da zaman dar-dar a Isra'ila yayin...

Alhazan Najeriya sun fara dawo wa daga ƙasar Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta sanar da isowar...

Sojoji sun kama ɗan kasar China da zargin kai wa ƴan Boko Haram kayayyaki

Rundunar sojojin ƙasar nan ta kama wani dan kasar...

Isra’ila ta tsokano tsuliyar Dodo – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya ce...

Da sani na Isra’ila ta kai hari Iran – Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa, yana sane...

Farashin man fetur ya tashi bayan Isra’ila ta kai wa Iran hari

Farashin man fetur a kasuwannin duniya ya tashi bayan...

Isra’ila ta kashe manyan Jami’an tsaron Iran su biyar

Wani hari da Isra'ila ta kira ‘Operation Rising Lion’,...

Isra’ila ta kashe Manyan Jami’an Iran biyar a hare-hare

Wani hari da Isra'ila ta kira ‘Operation Rising Lion’,...
X whatsapp