fidelitybank

Gwamnatin Legas za ta yi adalci a kan kisan Lauya

Date:

Gwamnatin jihar Legas ta dauki nauyin gurfanar da dan sandan da ya harbe Bolanle Raheem har lahira.

An kashe lauyan ce bayan da ASP Drambi Vandi ya bude wuta a ranar Kirsimeti bayan ya caccakar Bolanle da mijinta.

Vandi da tawagarsa, yanzu haka suna tsare, sun kasance a ofishin ‘yan sanda na Ajiwe da ke Ajah.

Kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) ta yi kira da a yi cikakken bayani kan abin da ya faru a ranar Lahadi.

A ranar Talata, Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya bayyana matsayinsa na yin adalci ga iyali.

Sanwo-Olu ya aika da tawagar manyan jami’ai domin ta’aziyyar ‘yan uwa a gidansu da ke Ajah.

Tawagar ta samu jagorancin babban lauya kuma kwamishinan shari’a Moyo Onigbanjo, SAN, wanda ya bayyana cewa jihar za ta gurfanar da shi gaban kotu.

“Muna da izinin Maigirma Gwamna mu gaya muku cewa za a yi adalci a wannan lamarin. Za a gurfanar da lamarin gaban kotu da zarar ‘yan sanda sun aiko mana da fayil din karar.

“Zan jagoranci masu gabatar da kara don nuna muhimmancin gwamnati game da wannan batu,” in ji Onigbanjo.

Mijin marigayi Bolanle, Gbenga Raheem ya godewa Sanwo-Olu kan yadda ya tausaya masa.

Sauran da ke cikin tawagar sun hada da shugaban ma’aikata Muri Okunola, kwamishinan mata da yaki da talauci, Bolaji Dada, kwamishinan yada labarai, Gbenga Omotoso, da kuma mai ba da shawara na musamman Tubosun Alake.

benue news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Na so komawa Manchester United a 2012 – Lwandowski

Ɗanwasan gaban ƙungiyar Barcelona ta Spain, Robert Lewandowski ya...

Isak ya dage sai ya koma Liverpool

Ɗanwasan gaba Alexander Isak ya nace sai ya bar...

Sadiq Umar da Bello El-Rufai sun sayi ƙungiyar Ranchers Bees ta Kaduna

Ɗanwasan tawagar Super Eagles ta Najeriya da Real Socieded...

Atiku zai iya guduwa daga ADC ya koma PDP idan Jonathan ya tsaya takara – Diran

Tsohon mataimakin sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na kasa,...

Zoben matar Ronaldo ya kai dala miliyan 5 – Masana

Masana sun yi kiyasin tsadar zoben da Cristiano Ronaldo...

Kama Tambuwal ya na da alaka da shigarsa cikin hadakar jam’iyya – Atiku

Tsohon ɗantakarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce kama...

Ambaliyar ruwa ta kashe mutuane takwas a Ebonyi

Ambaliya, wadda mamakon ruwan sama ya janyo, ta yi...

Bankin Duniya zai kashe wa yankin Arewa a Najeriya dala miliyan 300

Bankin Duniya ya amince da kasafin kuɗi dala miliyan...

Giyar mulki na kwasar Trump – ‘Yan Majalisar Democrat

'Yan Democrats a Amurka sun zargi Donald Trump da...

Kama Aminu Waziri Tambuwal da EFCC ta yi ba daidai ba ne – PDP

Jam'iyyar PDP a jihar Sokoto ta yi Allah-wadai da...

An kai hari a ƙauyuka 15 na Zamfara a mako ɗaya – Rahoto

Wani rahoto da tashar Channels ta ruwaito daga cibiyar Zamfara Circle...

Jihohin Arewa huɗu ne suke biyan mafi ƙarancin fansho na N32,000 – NUP

Ƙungiyar ƴan fansho na arewacin Najeriya, NUP ta ce...
X whatsapp