Yayinda yan Najeriya ke fama da matsanancin wahalar man fetur, an yi rabon jarkokin man a matsayin kyautar halartar biki a jihar Legas.
A wani hotunan bidiyon da wani @ThisIsKennys ya saki a shafinsa na Twitter, an kan yadda aka lika hotunan wanda ke bikin a jikin jarkuna da sunan “Erelu Okin Foundation Installation Party.”
Mawakin dake waka a taron ya jinjinawa wa matar da ke rabon fetur din, waddaa hadima ce ga Gwamnan jihar Ogun.
Sai dai gwamnatin jihar Legas a ranar Asabar ta bayyana cewa, ta na gudanar da bincike kan hoton bidiyon.
Ta kuma ce, “Ko shakka babu wannan abu na da hadari, kuma ya na iya zama musabbabin asarar rayuka da dukiya. Tsaron rayuka da dukiyoyin mutanen Legas na da muhimmanci ga gwamnatin Gwamna Babajide Sanwo-Olu.” A cewar ta.