fidelitybank

Gwamnatin Legas ta rufe kasuwannin jihar 13

Date:

Gwamnatin jihar Legas ta sanar da rufe wasu kasuwannin jihar 13, sakamakon saɓa doka kan zubar da shara ba bisa ƙa’ida ba.

Cikin wata sanarwa da kwamishinan Muhalli da albarkatun ruwan sha na jihar, Tokunbo Wahab ya wallafa a shafinsa na X, ranar Juma’a ya ce matakin ya zama wajibi domin tsaftace muhalli da inganta lafiyar al’ummar jihar.

Kwamishinan ya ce an ɗauki matakin ne bisa la’akari da dokokin kare muhalli na jihar da aka yi wa gyaran fuska a 2017, da nufin tabbatar da zuba shara a wuraren da suka dace da bin dokokin gwamnati.

Mafi yawan kasuwannin da aka rufe na yankunan Ketu da Mile 12 – waɗanda aka rufe jiya da daddare saboda ci gaba da saɓa doka, ciki har da zuba shara a kan hanyoyi da manyan titunan jihar.

Ga jerin kasuwannin da gwamnatin ta rufe kamar yadda kwamishinan ya wallafa a shafin nasa

  • Kasuwar Erukan da ke Mile 12
  • Kasuwar Oja Oba da ke Ketu
  • Kasuwar Owoseni Tundas
  • Kasuwar Oba Ogunjobi da ke Mile 12
  • Kasuwar Shops Owners (BRT Terminal) da ke Mile 12
  • Kasuwar tashar motoci ta Mile 12
  • Kasuwar Ketu Terminal (6 plazas)
  • Kasuwar Ifesowapo da ke Mile 12
  • Rukunin shagunan Demurin St Plaza, Ketu
  • Kasuwar The Occupant, da ke kan titin Demurin, Ketu
  • Kasuwar Ifelodun da ke Ketu
  • Kasuwar tashar Ibadan (da ke tsakanin kasuwar Babajide Sanwo-Olu da ta kayan gwari ta Ikosi)
  • Kasuwar Tipper Garage da ke Ketu

legit.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...

Tinubu ya haramta fitar da ɗanyen man kaɗanya

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin dakatar...

Hisba ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776 a Kano

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa, a...

Ganduje ba dan cin hanci ba ne – Martanin Garba Ga Gwamnatin Kano

Tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba,...

Kungiyar Malaman Jami’o’i bangaren BUK sun yi zanga-zangar Lumana

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK),...

An gargadi Borno da Yobe da Jigawa su zama cikin shirin ambaliya

Akwai yiwuwar samun ambaliya a jihohin Borno, Jigawa da...
X whatsapp