An bude wani karamin asibiti a kan ruwa a birnin Legas, wanda aikinsa shine bada agajin lafiya na gaggawa ga mazauna gabar ruwan birnin.
A ranar Laraba aka bude dakin shan maganin, wanda jami’ai suka ce, yana da ofisoshi da ma’aikatan jinya da sauran abubuwa masu muhimmanci a ciki.
A cewar babban sakataren ma’aikatar lafiya na jihar Legas, Olusegun Ogboye, makasudin bude dakin shan maganin a kan ruwa shine ”samar da agajin lafiya na gaggawa musamman ga al’ummar da ke makwabtaka da ruwan Legas.
Ya kara da cewa akwai anguwanni da dama a birnin Legas da ta hanyar ruwa kawai ake iya zuwan su.
Bugu da kari za a yi amfani da kwale-kwalen wurin ci gaba da yekuwar rigakafin kyanda da ta korona.
Wannan ne karon farko da aka samar da irin wannan dakin magani a Najeriya, kuma gwamnatin jihar Legas na shirin samar da wasu karin kwale-kwalen agajin lafiya a fadin jihar.