A ranar Alhamis din nan ne ma’aikatar shigar da kara ta jihar Legas (DPP), ta gurfanar da makarantar Chrisland School Ltd da wasu ma’aikata hudu a gaban kotu, bisa zargin kashe wata daliba mai shekaru 12 mai suna Whitney Adeniran.
An gurfanar da su a gaban mai shari’a Oyindamola Ogala na babbar kotun Ikeja.
Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa NAN, ya ruwaito cewa, Ademoye Adewale, Kuku Fatai, Belinda Amao, Nwatu Ugochi Victoria an gurfanar da su a gaban kuliya, bisa zarge-zarge biyu da suka hada da kisan kai da kuma sakaci.
Sai dai wadanda ake tuhumar sun ki amsa laifin da ake tuhumarsu da shi bayan an karanta musu.