fidelitybank

Gwamnatin Legas ta fara bincike a kan korar daliba saboda Obi

Date:

Gwamnatin jihar Lagos ta fara gudanar da bincike kan zargin da ake yi cewa, wani shugaban makaranta ya kori ɗaliba saboda ta naɗe bangon littafinta da hoton ɗan takarar shugabn ƙasa na jam’iyyar Labour Peter Obi.

A wata sanarwa da mataimakin darektan hulɗa da jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar, Ganiu Lawal, ya fitar ya ce, gwamnati ta gayyaci shugaban makarantar inda za ta nemi ya yi bayani kan lamarin.

Karanta Wannan: Ina da kwarin gwiwa kotu za ta kwato min kujera ta a wajen Tinubu – Obi

Mahaifiyar ɗalibar ta sanya labarin abin da ta ce ya faru da ƴar tata mai shekara 10 ne a shafin sada zumunta da muhawara, wanda hakan ya sa labarin ya bazu ake ta ce-ce-ku-ce a kai, har gwamnati ta ɗauki matakin binciken.

Kwamishinar ilimi ta jihar ta Lagos Mrs Folashade Adefisayo a sanarwar ta bai wa jama’a tabbacin cewa za a ɗauki matakin da ya dace kan lamarin bisa abin da doka ta tanada, domin a cewarta dalilin korar yarinyar ba abin da za a lamunta ba ne, idan har ya tabbata hakan.

A ranar Talata ne rahotanni labarin ya bayyana cewa shugaban ƙaramar sakandire ta Odomola, da ke Epe a Lagos ya kori ɗaliba Marvellous Barinaadaa zuwa gida saboda ta nade bangon littafinta da hoton Peter Obim, wato ɗan takarar jam’iyyar Labour, da ya zo na uku a sakamakon zaɓen shugaban Najeriyar da hukuma ta bayyana.

www nnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp