Gwamnatin jihar Legas ta bada umarnin bude dukkan makarantun Chrisland.
Ku tuna cewa gwamnatin jihar ta rufe dukkan makarantun Chrisland da ke jihar Legas a ranar 18 ga Afrilu, 2022, saboda cece-kucen da ya dabaibaye wani lalata da wasu daliban makarantar suka yi.
A cikin wata sanarwar manema labarai da kwamishinan ilimi na jihar Legas, Mrs Folasade Adefisayo, ta fitar, ta ce, “Ma’aikatar ilimi ta jihar Legas ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun Chrisland bisa zargin rashin da’a a Dubai daga ranar Litinin 25 ga Afrilu, 2022.