Gwamnatin jihar Kuros Riba na shirin siyan sharar gida daga wajen jama’a musamman wadanda ke cikin birane.
Babban Manajan Hukumar Kula da Sharar ta Jihar, Sunny Uko ya bayyana hakan a wani taron da kungiyar Injiniyoyi ta Najeriya ta shirya a Calabar.
A cikin watanni hudu da suka gabata, zubar da shara ya zama babban kalubale ga gwamnatin jihar, inda tsaunuka suka toshe manyan tituna.
A wajen taron, Uko ya ce shirin shi ne a rika siyan sharar gida daga wajen mutanen da galibi ba sa biyan kudaden kwashe mutanen.
“Muna da shirin sayan sharar gida daga mazauna jihar.
“Za mu rika bi gida-gida don tantancewa da siyan su,” in ji shi.