Rahotonnin da ke fitowa daga Koriya ta Kudu na cewa mutum 179 ne suka mutu a hatsarin jirgin saman da ya auku a filin jirgin saman Muan ranar Lahadi da safe.
Mutum biyu kawai aka samu cetowa daga hatsarin – waɗanda dukkansu ma’aikatan jirgin ne da aka zaƙulo daga cikin baraguzan jirgin.
Hakan na nufin duka fasinjojin jirgin 175 haɗe da ma’aikatansa hudu sun mutu a hatsarin.
Gwamnatin ƙasar Koriya ta Kudu ayyana makokin kwana bakwai, domin jimamin mutanen da suka mutu a hatsarin jirgin sama.
Za a sauko da tutocin ƙasar ƙasa-ƙasa, yayin da ma’aikatan gwamnati za su ɗaura baƙin ƙyalle a tufafinsu a tsawon kwanakin.