fidelitybank

Gwamnatin Kogi ta rufe kamfanin sadarwa na Glo da Airtel

Date:

Hukumar tattara kudaden shiga ta jihar Kogi (KGIRS), ta ce, ta rufe cibiyoyin sadarwa na Globacom da Airtel, saboda gaza biyan harajin sama da Naira miliyan 360.

Saidu Okino, darakta mai kula da harkokin shari’a da tabbatar da doka na KGSIRS, ya jagoranci tawagar jami’an tsaro wajen rufe wuraren da ke Dutsen Patti a Lokoja da kuma fadin jihar.

Mista Okino, wanda ya samu wakilcin shugaban sashen tabbatar da tsaro na ma’aikatar kudaden shiga, Abubakar Obori, ya koka da yadda kamfanonin sadarwar biyu suka ki biyan harajin da ya rataya a wuyan jihar.

Ya ce, “Abin takaici ne yadda kamfanonin biyu suka ci gaba da kaucewa biyan bukatunsu ga jihar, kuma sun tara bashin Naira 360,035,000.00,” in ji Mista Okino.

“A bayanin mu, Globacom Nigeria Ltd., jihar Kogi, harajin da ba a biya ba, ya kai Naira miliyan 300,000,000, yayin da na Airtel ya kai Naira miliyan 60,035,000. Waɗannan alawus-alawus na kamfanonin biyu da suka yi kasala wajen biya mun rufe duka kamfanoni”.

Mista Okino ya kara da bayyana cewa, an rubuta “wasiku da dama” ga kamfanonin biyu, domin su kwantar da hankulan su don biyan harajin da suke bin gwamnatin Kogi, “amma ba su taba nuna wata alama ba.

Ya bayyana cewa rufe shafuka da kadarori na kamfanonin sadarwa ya kasance bisa umarnin kotu.

Mista Okino ya gargadi sauran kamfanonin da ke aiki a jihar da su rinka biyan kudaden harajin da ake bin su a kodayaushe, domin kaucewa fushin doka.

nigeria 
news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp