Gwamnatin jihar Kebbi ta bayar da umarnin rufe kwalejin kiwon lafiya ta Jega, bayan zanga-zanga da ɗalibai suka yi wanda ya rikiɗe zuwa tarzoma.
Kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar, Isah Abubakar Tunga ne ya sanar da haka ga manema labarai, inda ya ce ɗaukar matakin ya zama wajibi domin kaucewa yaɗuwar rikicin.
Ɗaliban sun ce sun shiga zanga-zangar ne domin nuna fushinsu kan rashin yi wa wasu kwasa-kwasai rajista, rashin kyawun wurin zama da kuma rashin shugabanci na gari.
An nuna wasu ɗalibai sun far wa gidan shugaban kwalejin, inda suka cinna wa gidansa wuta da kuma lalata motarsa.
Tunga ya tabbatar da cewa za a kafa wani kwamiti domin gudanar da bincike kan lamarin.
Ya kuma ce za a hukunta duk wanda aka samu da hannu a lamarin.
Yanzu dai kwalejin zai ci gaba da zama a rufe har na tsawon makonni uku, a cewar gwamnatin jihar.