Gwamnatin jihar Katsina ta c,e za ta raba shinkafa ga tsofaffi da masu bukata ta musamman da ma gajiyayyu kimanin 33,000 a fain jihar.
Cikin wani sako da gwamnan jihar Dikko Umaru Radda ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce a kokaruin da gwamnatinsa ke yi magance matsin rayuwa da tsadar hatsi, gwamnatin jihar za ta raba hatsi a kan farashi mai rahusa da za a sayar kan kudi naira 20,000 kowane buhu, don agaza wa masu karamin karfi a jihar.
”Hatsin da za a sayar kan wannan farashin su ne masara, gero, da dawa”, in ji sanarwar.
Gwamnan ya ce kowane dan jihar na da damar sayen mudu (tiya) goma na hatsin kuma kowace tiya daya, za a sayar da ita kan kudi naira 500, idan aka kwatanta da farashin kasuwa a yanzu da ake sayarwa kusan naira 1,500, kamar yadda sanarwar ta yi bayani.
Gwamna Radda ya kuma ce gwamnati za ta rika daukar nauyin dafa abinci a kowace rana cikin watan azumin Ramadan a fadin duka mazabun jihar 361 domin rage wahalhalun da tsadar rayuwa da al’ummar kasa ke fuskanta.
”Bugu da kari, za a yi kokarin tallafa wa manoma da karfafa aikin noma domin rage dogaro da hanyoyin samar da abinci daga waje”, in ji gwamnan.
Tun bayan cire tallafin man fetur a shekarar da ta gabata dai shugaban kasar Bola Tinubu ya bukaci gwamnonin jihohin kasar su rika bullo da sabbin hanyoyin tallafa wa talakawan kasar don rage musu radadi.


 

 
 