Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, ya ayyana ranar Juma’a 29 ga watan Yuli a matsayin ranar da babu aiki ga ma’aikata, domin karbar katin zabe na dindindin.
Babban sakataren dindindin na ofishin gudanarwa na babban ma’aikata, Alhaji Usman Isyaku ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai a Katsina ranar Alhamis.
Sai dai sanarwar ta bayyana cewa hutun bai shafi muhimman ma’aikata irin su Ma’aikatan Banki, Ma’aikatan Lafiya, ‘Yan Jarida da Ma’aikatan Hukumar Ruwa ta Jihar ba.
Hakazalika, an yi kira ga Shuwagabannin Makarantun Sakandare da su kwadaitar da daliban da suka cancanta da suke rubuta Jarrabawar SSCE da su yi rijista don samun katin zabe na dindindin.
“An yi kira ga duk masu kada kuri’a da su ziyarci wuraren rajista mafi kusa don karbar katin zabe domin su samu damar shiga zaben 2023,” in ji ta.