fidelitybank

Gwamnatin Kano za ta yi wa yara miliyan 3.6 rigakafin shan inna

Date:

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano, ta kammala shirin yi wa yara miliyan 3.6 allurar rigakafin cutar shan inna ta novel type 2 ta baki (nOPV2) a wani mataki na mayar da martani ga barkewar cutar poliovirus mai saurin yaduwa a jihar.

A cikin lokaci guda ne dai, ma’aikatar ta kaddamar da shirin makon kiwon lafiyar jarirai da mata masu juna biyu (MNCHW), domin rage yawan mace-macen da ake samu, inda za a kashe sama da Naira biliyan 2.5 wajen gudanar da ayyukan biyu.

Da ya ke jawabi ga manema labarai a ranar Juma’a, kwamishinan lafiya na jihar, Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa ya bayyana cewa, hadaddiyar kamfen na OBRI da MNCHW za su gudana ne a lokaci guda daga ranakun 9 ga Alhamis 13 ga watan Janairu 2022.

Dr. Tsanyawa ya yi bayanin cewa, ingantattun allurar rigakafin cutar shan inna ta zama dole, domin samun nasarar kawar da cutar shan inna ta duniya (GPEI).

Kwamishinan ya yi nadamar cewa shekaru uku bayan da Najeriya ta samu kasar da ba ta da cutar shan inna, an gano bullar cutar shan inna mai nau’in 2 (cVDPV2) a jihohi 13 na tarayyar kasar ciki har da Kano tare da samun mutum 106 da suka kamu da cutar a fadin kananan hukumomin 25.

Dr. Tsanyawa ya kuma yi kira ga iyaye tare da mata masu juna biyu da su yi amfani da wannan damar na samar da lafiyar ƴaƴan su.

hausa news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp