fidelitybank

Gwamnatin Kano za ta fara daukar mataki a kan masu zubar da shara – REMASAB

Date:

Hukumar kwashe shara REMASAB ta jihar Kano, ta ce za ta fara daukar mataki kan duk mai shagon da baya zuba shara a muhallin da gwamnatin ta kebe a kasuwannin jihar.

Wannnan na zuwa ne ya yin da hukumar ta ce ta lura wasu ‘yan kasuwar na zuba shara a wuraren da ba su kamata ba, al’amarin da yasa sharar ke taruwa ta cunkushe hanyoyi.

REMASAB ta sanar da cewa nan gaba kadan za a ɓullo da wani shiri da zai tilasta wa masu shaguna da motocin haya saka kwandon shara a cikin mota da wuraren kasuwanci.

Shugaban hukumar Alhaji Ahmadu Haruna Zago, ya shaida wa BBC cewa, bayanan da suka samu akwai wuraren kasuwanci da dama a sassan jihar, da ake zuba shara-barka-tai, al’amarin da yace ba za su lamunta ba.

Ahmadu Zago, ya ce za su kalli dokokin hukumar kwashe shara da dokokin jiha da na kasa wadanda suka yi tanade-tanade game da irin wadannan matsaloli wajen yin hukunci.

Jihar Kano wadda ke kan gaba wajen yawan al’umma a arewacin Najeriya, na fama da matsalar shara, inda a wasu unguwanni wari da hayaki ke addabar jama’a da kuma barazanar ambaliya saboda cushewar magudanan ruwa.

punch newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp