fidelitybank

Gwamnatin Kano Tinubu ya ce har yanzu ni ne shugaban APC – Ganduje

Date:

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa wanda mazaɓarsa ta ce ta dakatar da shi, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin Jihar Kano ba ta isa ta ƙwace kujerarsa ba, yana mai cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu da kansa ne ya tabbatar masa cewa “kujerarsa na nan daram-dam.

Ganduje ya bayyana haka ne a wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke nuna shi yana jawabi ga dandazon magoya bayansa da suka kai masa ziyara a gidansa na Abuja domin nuna goyon baya.

Ya ce “jiya na ga shugaban ƙasa, Bola Tinubu kuma na yi masa bayanin komai kuma ya gode muku abin da kuka yi.” in ji Ganduje yayin da yake magana ga magoya bayansa.

“Sannan shugaban ya ce ku yi hakuri, wannan kujerar da suke hari, kujerar tana nan ta zauna daram-dam.” in ji Ganduje.

Tsohon gwamnan ya kuma ce Tinubu ya tabbatar masa da cewa kujerar shugabancin jam’iyyar APC ta Najeriya tasa ce kamar yadda ya faɗa “kujerar shugabancin APC ta Najeriya tana kan Abdullahi Umar Ganduje.”

An nuna magoya bayansa a cikin bidiyon suna ta murna da shewa da tafi yayin da tsohon gwamnan ke gabatar da kalamansa.

A yau Laraba ne dai wata babbar kotu a jihar Kano ta dakatar da Ganduje daga shugabancin jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya bayan wasu shugabannin APC tara a mazaɓar ta Ganduje suka shigar da ƙara kan a dakatar da shi bayan wata takardar koke da wani ɗan jam’iyyar Ja’afaru Adamu ya shigar.

A takardar koken, Adamu ya yi magana kan tuhume-tuhumen rashawa da ake yi wa tsohon gwamnan inda ya buƙaci jagororin mazaɓar su gudanar da bincike kan batun domin farfaɗo da ƙimar jam’iyyar da kuma tasirin da batun zai yi a fafutukar gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta yaƙi da rashawa.

the punch newspaper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp