fidelitybank

Gwamnatin Kano ta yi gargadi a kan tirka-tirkar Tik-Tok da a ke yi

Date:

Gwamnatin jihar Kano ta yi wa Malaman addinin Musulunci gargadi da masu amfani da shafukan sada zumunta da su lura da abin da suke faɗa, domin harshe ka iya kai su ya baro su.

Cikin wani hoton bidiyo na minti biyar da kwamishinan addinai na jihar Muhammad Tahar Adam Baba Impossible ya yi, ya bayyana matsayar gwamnatin Jihar Kano kan ce-ce-ku-cen da ya ɓarke bayan yaɗuwar wani bidiyo da Sheikh Daurawa ke magana a kan al’aurar mata da kuma martanin da Nafisa Ishak wata mai amfani da shafin Tiktok ta yi.

A makon da ya gabata ne Sheikh Daurawa a wani bidiyo aka ji yana ba da misali da yadda al’aurar mata ke da muni duk da cewa yana cikin ƙwace-ƙawacen duniya.

Hakan ya sa mutane suka yi ta mayar da martani daga ɓangarori daban-daban, sai dai mafi jan hankali shi ne na wata mai amfani da shafin Tiktok Nafisa wacce ta yi “kakkausan martani” ga Malam Daurawan.

Daga baya kuma wani malamin mai suna Asadus Sunnah ya yi nasa bidiyon yana gargaɗin Nafisan tare da yin barazanar cewa suna da yaran da za su tura su yi maganinta.

Kwamishinan addinan ya shaidawa BBC abin da ya sa gwamnati ba ta yi magana tun da farkon lamarin ba, saboda ta tsaya tattara bayanai ne daga ɓangarorin kafin yanke hukunci.

Baba Impossible ya fara da bayani ne kan cewa Malam Daurawa bai yi dai-dai ba kan bayanan da ya yi, yayin wani karatu a ranar Litinin wanda yake yi kullum.

“Gwamnatin jihar Kano ta ji ta kuma saurari abubuwan da ke faruwa duka, ta tambayi malamai da masana, an kuma ji bangarori daban-daban kuma an kalli jawabin kowa.

“Abin da ma’aikata ta tsaya a kansa, kamar yadda muka ji daga bakin malamai, shi mai jawabi na farko ya yi kuskure a jawabinsa, kamata ya yi ya tsaya kan Ƙala Allahu ƙala Rasulihi.

“Idan akwai wani ƙarin bayani kar a yi shi cikin yadda zai yamutsa hazo yadda zai ta da ƙura, yadda zai tayar da hankalin mutane yadda zai zama kamar akwai batsa, kamar akwai cin mutunci, kamata ya yi a saya shi.

“Don haka tun a nan muka fuskanci akwai kuskure a jawabin da ya yi,” in ji Baba Impossible.

Ya ci gaba da cewa malami ba ma’asumi ba ne zai iya yin kuskure, don haka idan malami ya yi kuskure ya iya gyarawa.

Cikin bayanansa ya riƙa kin ambatar sunan Malam Aminu Daurawa, inda ya riƙa siffanta shi da mai magana na farko ko kuma mai wa’azi.

Da yake bayani a kan Nafisa Ishak, Kwamishinan ya ce ita ma a jawabanta akwai kuskure masu yawa kuma sun yi nazari kansu.

“Ba ta cikin rukunin wadanda za su iya mayar wa da Malamin martani, idan malami ya yi maganar malami dan uwansa ya kamata ya mayar masa da martani idan da kuskure ya fada masa cewa bai yi dai-dai ba ya gyara.

“Amma ba ita da take matar wani ko budurwa ko bazawara ba.

“Maganganun da ta yi sun yi tsauri, don haka ba mu yarda da abin da ta fada ba, ba dai-dai ba ne, ko da yake dai ba zagi ba ne kai tsaye, amma zagi ne idan aka kalli yadda ta furta su,” in ji Kwamishinan addinan.

vanguard news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...
X whatsapp