fidelitybank

Gwamnatin Kano ta tabbatar da yaduwar wasu cututtuka da aka yi watsi da su

Date:

Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da bullar cututtuka biyar da aka yi watsi da su daga cikin 20 da aka ce suna yaduwa a fadin kasar nan.

Kwamishinan lafiya na jihar Dr Aminu Tsanyawa ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai na bikin ranar amsu lalurar cutar kuturta ta duniya.

Kwamishinan wanda ya samu wakilcin babban sakatare a ma’aikatar, ya bayyana cewa, ana gudanar da wannan rana ne a duk ranar Lahadin da ta gabata na watan Janairun kowace shekara, a daidai lokacin da Mahatma Gandhi ya mutu, a wani taron tunawa da tallafin da ya baiwa masu fama da kutare a duniya.

“An ware taron ne domin wayar da kan jama’a cewa, har yanzu kuturu da sauran NTDs na nan a waje kuma suna yin barazana ga lafiyar jama’a da ke shafar lafiyar jiki, tunani da tattalin arzikin wadanda abin ya shafa tare da kawo karshen kyama da nuna wariya ga mutanen da abin ya shafa a duniya.” In jiTsanyawa.

A kwanakin baya ne ma’aikatar lafiya ta tarayya ta bayyana cewa, Najeriya ta na fama da cutar guda 15 daga cikin 20 NTDs da Hukumar Lafiya ta Duniya ta lissafa, kuma ta yi kira da a kawo dauki cikin gaggawa, domin dakile illolin da ke tattare da cututtuka.

legit latest news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Mutane 12 sun mutu a wani hatsari a Kano – FRSC

Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC) reshen Kano, ta...

Masarutar Rano ta haramta aurar da Yaran da ba su kammala karatun Firamare ba

Masarautar Rano a Kano ta haramta cire yarinya daga...

Matatar Dangote za ta fara jigilar mai kyauta ga gidajen mai

Matatar man Dangote za ta fara jigilar mai kyauta...

An sassata rikicin da aka shafe shekaru 30 kan Masallacin Sharada da Islamiyya

Tsohon dan takarar gwamnan Kano, Malam Sha’aban Ibrahim Sharada,...

Duk da kalubalen ‘yan siyasa a Kano mun shirya a zaben cike gurbi – INEC

Kwamishinan hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) reshen jihar...

Barau ya jagorancin gangamin zaben cike gurbi a Kano

Barau ya samu rakiyar Karamin Ministan Gidaje da Raya...

Gwamnatin Kano ta kara fadada shirin matasa 

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya sake,...

An kaiwa Malamin addini hari a Kano bayan an jikatasu da Matarsa

Wani malamin addinin Musulunci, Malam Kabir Idris, da matarsa...

Kotun Kano ta daure wata Mata da ake zargin ta tsafe su

Kotun Majistiri mai lamba 7 da ke Nomansland, ƙarƙashin...

Dalibi ya kashe kansa a cikin Jami’a

Hukumar jami'ar Obafemi Awolowo da ke jihar Osun, sun...

Gobara na cigaba da lakume wasu yankunan Turai

Gobarar daji na ci gaba da ruruwa a sassan...

An kama Fursunoni 7 da suka tsere daga gidan kurkukun jihar Nasarawa

Hukumar kula da gidajen yari a Najeriya ta ce...
X whatsapp