fidelitybank

Gwamnatin Kano ta sallami ‘yan Jaridu 14

Date:

Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da ‘ƴan jarida 14 da ke aiki a fadar gwamnatin jihar daga aiki tare da neman sauyinsu daga hukumomin da suke ƙarƙashinsu.

A wani saƙo da kakakin gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ga waɗanda abin ya shafa, ya umarce su da su koma wuraren aikinsu, tare da neman hukumominsu su aika da wasu da za su maye gurbinsu a gidan gwamnatin jihar.

Babu wani dalili da kakakin ya bayyana na ɗaukar wannan mataki, illa dai ya buƙace su da su bi umarnin wanda ya fara aiki daga yau Talata.

To amma a saƙon da ya rubuta a shafin WhatsApp na tawagar ‘yanjaridar da ke aiki a fadar gwamnatin jihar ta Kano, Sanusin ya bayyana cewa : ”Abin takaici a lokacin da na yi tafiya zuwa ƙasar Serbia a makon da ya gabata, wasu abubuwa sun faru, saboda haka akwai buƙatar shugabancin a wannan mawuyacin hali ya ɗauki mataki…”

Wasu daga cikin ƴanjaridar da abin ya shafa sun haɗa da na kafofin yaɗa labarai na gwamnatin jihar da na tarayya da kuma masu zaman kansu.

Daga cikinsu akwai daraktan wayar da kan al’umma, Aliyu Yusuf da jimi’im hulda da jama’a, Sani Suraj Abubakar da Adamu Dabo da ke kai rahoto ga gidan rediyon Pyramid (FRCN). Sai kuma Naziru Yau daga ARTV da Sadiq Sani AA daga ARTV da Rabiu Sunusi da Umar Sheka daga rediyon Freedom, cewar Premium Times. Har ila yau, akwai Jabir Dan’abba daga gidan rediyon Nasara sai Labara Sound da Simon daga AIT sai Nasiru Danhaki daga NTA da direbansu, Abdullahi Sule da Murtala Baba Kusa daga gidan rediyon Express da Ibrahim Muazzam daga rediyon Kano.

naija news legit

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp