Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya sake, tabbatar da kudurin gwamnatinsa na karfafa matasa ta hanyar samar da ayyukan yi masu ɗorewa, fadada damar koyon sana’o’i, da kuma ƙarfafa yaki da amfani da miyagun kwayoyi.
Gwamnan ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Laraba, domin tunawa da Ranar Matasa ta Duniya a wannan shekara.
“Matasa su ne ginshiƙin canjin tattalin arziki da zamantakewa a Kano,” in ji Gwamna Yusuf. “Mun sake buɗe cibiyoyin koyon sana’o’i a fannoni daban-daban, wanda hakan ya ba dubban matasanmu damar dogaro da kansu.”
Haka kuma, an samar da damar aiki kai tsaye a muhimman sassa kamar kiwon lafiya, ilimi, aikin gona, da ayyukan gwamnati.
Gwamnan ya kuma bayyana shirin sake buɗe Cibiyar Gyara Hali na Kiru domin gyara da dawo da matasa masu laifi musamman waɗanda ke fama da amfani da miyagun kwayoyi.
A bangaren Fasahar Sadarwa da Kwamfuta (ICT), Yusuf ya jaddada nasarorin da aka samu ta kafuwar Hukumar KASITDA da kuma nasarar shirya Taron Kasa da Kasa kan Fasaha da Kwamfuta.
Ya bayyana waɗannan a matsayin muhimman matakai don sanya Kano cibiyar ƙirƙira da kwarewar dijital.
“A wannan Ranar Matasa ta Duniya, muna murnar juriya, ƙirƙira, da ƙarfin matasanmu,” in ji gwamnan. “Gwamnatina za ta ci gaba da zuba jari a makomar su ta hanyar samar da ayyukan yi, ilimi, fasaha, da yaki da miyagun kwayoyi.”
Gwamna Yusuf ya yi kira ga shugabannin al’umma, malamai, iyaye, sassan masu zaman kansu, da sauran masu ruwa da tsaki su haɗa kai wajen samar da yanayi mai aminci, haɗin kai, da wadata domin matasan Kano su cika burinsu cikin cikakken iko.