fidelitybank

Gwamnatin Kano ta kai Buhari kotu akan sauyin kudi

Date:

Gwamnatin Jihar kano ta kai gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kara a gaban Kotun Kolin kasar nan, a kan sauyin fasalin wasu daga cikin manyan kudin kasar na naira 200 da 500 da 1,000.

A karar wadda Babban Lauyan jihar ta Kano ya shigar ta hannun Sunusi Musa babban lauya a Najeriya (SAN), a jiya Alhamis, gwamnatin tana bukatar kotun ta ayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari shi kadai ba shi da hurumin umartar Babban Bankin Kasar, CBN ya dakatar da amfani da takardun kudin na naira 200 da 500 da kuma 1,000 ba tare da tuntuba da amincewar majalisar tattalin arziki da kuma majalisar zartarwa ta kasar ba.

A don haka ne gwamnatin jihar ta Kano take son Kotun ta soke matakin Babban Bankin na Najeriya na janye takardun kudaden saboda abin ta kira wahalar da al’ummar jihar ke ciki asaboda matakin na CBN.

A tattaunawarsa da BBC lauyan da ya shigar da karar Sunusi Musa ya ce a ranar Laraba ne Kotun za ta saurari karar.

Harwayau gwamnatin tana son kotun ta bayar da umarnin da zai tilasta wa gwamnati ta soke shirin nata na sauyin kudi saboda a cewarta ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar na 1999.

A karar gwamnatin jihar ta Kano tana kuma bukatar Kotun Kolin ta zartar cewa umarnin da Shugaba Buhari ya bai wa Babban bankin Kasar na takaita yawan kudin da jama’a za su fitar daga asusunsu na banki ba tare da tuntubar majalisar tattalin arziki da kuma ta zartarwa ba, abu ne da ya saba wa tsarin mulki da saba wa doka a don haka ba shi da iko.

Kafin wannan daman gwamnonin jihohin Kaduna da Zamfara da Kogi sun shigar da kara kan batun, har Kotun Kolin ta dakatar da Babban Bankin Najeriyar aiwatar da wa’adin da ya sa na daina amfani da takardun kudin na ranar 10 ga watan nan na Fabarairu wato yau, Juma’a, har sai ta yanke hukunci a ranar 15 ga watan na Fabarairu na 2023.

punch newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp