Gwamnatin jihar Kano ta amince da kundin tsarin mulki na kwamitin mutane 22 da za su tafiyar da harkokin hukumar Hisbah ta jihar.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, wanda ya bayyana hakan a cikin sanarwar, ya ce, amincewar ta biyo bayan shawarar kwamitin da aka kafa, domin duba ayyukan hukumar da kuma yin daidai da dokar jihar.
Ya ce. rahoton kwamitin ya ba da shawarar kafa hukumar kuma an gabatar da shi a gaban majalisar zartarwa ta jihar wadda ta ba da amincewa.
Malam Garba ya bayyana cewa, hukumar wadda aka zabo ta a tsanake bisa la’akari da iya aiki da cancantar su, ta na da Sheikh Ibrahim Shehu Maihula a matsayin shugaba.
Kwamishinan ya kara da cewa, sauran mambobin hukumar sun hada da Ustaz Muhammad Haroun Ibn Sina, babban darakta na hukumar Hisbah; Wakilin Majalisar Masarautar Kano, Daraktan Ma’aikatan Jiha, ‘Yan sanda da Hukumar Tsaro ta Civil Defence, Hukumar Shige da Fice ta Kasa, Wakilan Ma’aikatar Shari’a ta Jiha, Ofishin Majalisar Zartaswa, da dai sauransu.
Ya kuma bayyana cewa, an kuma amince da nadin Alhaji Abdullahi Balarabe, wanda ya yi murabus sakataren dindindin a babban daraktan ma’aikatan gwamnati na jiha.


