Gwamnatin jihar Kano sanar da matakin haramta zirga-zirgar baburan A daidaita sahu a kan wasu manyan hanyoyin jihar.
A wata sanarwa ta hannun Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar (KAROTA), gwamnatin ta ce wannan doka za ta fara aiki ne daga ranar Laraba, 30 ga watan Nuwamba, 2022.
Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne bayan da ta samar da manyan motocin da za su rinƙa ɗaukar al’umma a titinan da aka haramta wa ƴan A daidaita Sahun.
Hanyoyin da aka haramta wa baburan masu ƙafa uku su ne Ahmadu Bello By Munduɓawa zuwa Gazawa, da titin Tal’udu zuwa Gwarzo.
Sanarwar ta kuma ce za a bayyana ranar da masu A daidaita sahun za su daina bin wasu ƙarin manyan tituna na birnin.