Gwamnatin jihar Kano ta sanar da cewa manyan motocin daukar kaya za su daina shigowa cikin birnin Kano da rana, domin rage cunkoson ababen hawa da kuma bunkasa tsaro a jihar .
Kwamishinan Sufuri na Jihar Muhammad Ibrahim Diggol, ne ya bayyana hakan, yayin tattaunawarsa da Kafar yada Labarai a Kano.
Wannan mataki yana daga cikin kudurorin gwamnati na tabbatar da kyakkyawan tsarin sufuri a jihar.
Wannan dokar za ta fara aiki nan ba da jimawa ba, inda aka tsayar da lokacin da motocin daukar kaya za su iya shigowa da kuma fita daga birnin.
Ana sa ran wannan tsari zai rage wahalhalun tafiye-tafiye ga ‘yan gari da kuma kare muhalli daga matsalolin da cunkoso ke haifarwa.