Gwamnatin jihar Kano ta ce, a wani mataki na kokarin kare tarbiyar yara ɗalibai, ta haramta amfani da wasu litattafan koyarwa a makarantun nazari da firamare da kuma sakandare a faɗin jihar.
Matakin ya zo ne a matsayin martani game da damuwar da aka nuna kan cewa an saƙala wasu abubuwa na “batsa wadanda ke yin illa ga tarbiyyar yara ƴan makaranta.”
Sanarwar haramcin na ƙunshe ne cikin wani bayani da ya fito daga ofishin mai bai wa gwamna shawara kan makarantu masu zaman kansu a ranar Juma’a.
Littattafan da aka dakatar sun hada da ‘The Queen Primer’ da ‘Basic Science for Junior Secondary School” published by Razat Publishers, 2018 editon’ da “Active Basic Science 2014 edition by Tora Ajorin and others’
Sauran sun hada da; “Basic Science and Technology for Junior Secondary School 1, 2, da 3” na W.K Hamza da Bakare’ da kuma “New Concept English for Senior Secondary Schools for JSS 2” a cikin edition na 2018 wanda J. Eyisi da A. Adekunle suka rubuta’.