Gwamnatin jihar Kano ta sanar da hana zirga-zirgar babura masu kafa uku, wanda da aka fi sani da Adaidata Sahu, bayan karfe 10:00 na dare daga ranar Alhamis 20 ga watan Yuli, 2022.
Kwamishinan yada labarai, Malam Muhammad Garba ya fitar ta nuna cewa an cimma matsaya kan hakan ne a karshen taron Majalisar tsaro ta jihar Kano.
Ya ce, matakin wani bangare ne na kokarin tabbatar kare rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar.
Kwamishinan, a cikin sanarwar, ya bukaci masu tuka baburan da su bi umarnin, kuma su daina aiki a lokacin da aka kayyade, domin jami’an tsaro za su aiwatar da dokar ba tare da wata matsala ba.